Ƙara kuɗin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja rashin tausayi ne – Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya a zauren majalisar dattawan ƙasar nan, Shehu Sani ya gargadi ma’aikatan sufuri da kada su kuskura su kara kudin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja kamar yadda aka sanar.


Tun da farko wasu rahotanni sun rawaito ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa za a kara kudin sufurin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja saboda yadda za a rage yawan wadanda za su rika shiga a dalilin annobar Korona.


“Akwai yiwuwar za a kara kudin jirgin kasa. Babban dalili kuwa shi ne, maimakon mutum 88 da kowanne tarago yake dauka yanzu mutum 40 ne kacal zai dauka saboda haka dole kudin ya karu, wato ya kusa rubunyawa ma” 


Amaechi ya ce ba za su ɗauki wannan mataki ba sai sun shawarci shugaban ƙasa kuma ya basu amincewar ayi haka.

Sai dai kuma Sanata Shehu Sani ya kushe wannan mataki da gwamnati ke so ta dauka game da karin kudin sufurin jirgin.

“Yanzu fa titunan mu a arewa sun koma hannu ‘yan bindiga, masu garkuwa da kuma mahara. Jirgin ne mafita a gare mu, idan aka kara kudin jirgin yaya mutane za su yi, domin nan ne kawai ya rage ake dan samu a bi.

Idan kudin shiga jirgin yayi tsada, yaya talaka zai yi da rayuwar sa, a wannan yanayi da ‘yan ta’adda, mahara da masu garkuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *