Sojoji Sun Halaka Wasu Daga Cikin ‘Yan Bindigar Da Suka Addabi Kauyukar Jihohin Sokoto, Zamfara Da Katsina (hotuna)

Rundunar sojojin Najeriya na cigaba da samun gagarumar nasara a yunkurinsu na ganin sun kakkafe ‘yan bindiga da suka addabi wadan nan jihohi daga doron kasa, dakarun sojojin Operation Hadarin Daji, da Operation Sahel, sun gudanar da hare-hare a kauyuka da dama na jihohin Zamfara,Sokoto da Katsina.

Sun kai hare-hare a mabuyar Yan bindigar inda suka kashe ‘yan bindiga da dama tare da kwato Shanu 121 da Tumaki 37 a garin Dan jibga da ke cikin karamar Hukumar tsafe dake jihar Zamfara.

Haka Zalika jigiwar malami a karama Hukumar Dan musa da ke cikin jihar Katsina, dakarun sojojin Najeriya sun hallaka Yan ta’adda tare da Kona maboyarsu kwara 21.

Haka zalika sojojin Najeriya sun hallaka ‘Yan bingigar Garin maza, Tamuske, Dan kaka, Dan kura da garin Bagwari duka a cikin karama Hukumar Sabon Birni da ke jihar sokoto. Dakarun sojin suyi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama tare da Kona moboyarsu da kwato bindigogi Kira Ak47.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *