Ruguntsumin Neman Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Kara Kamari A Jihar Neja

Ruguntsumin Neman Shugabanci a jam’iyar PDP na kara kamari a jihar Neja. Inda tsohon Gwamnan Jihar ya gayyaci shugabannin kananan hukumomi 25 Dake Fadin Jihar.

Amma guda 5 kacal suka amsa Gayyatar, Rashin Amsa Gayyatar Da Sauran Shugabannin Basuyi Ba, Ya janyo Cece-kuce A Sakanin Membobin Jam’iyya.

Shugaban Jam’iyar na rikon kwarya ya rubutawa ciyamomin, takardar tuhuma kan rashin amsa gayatar ta tsohon Gwamnan.

Inda wasu suke ganin Rashin Amsa Gayyatar ya kasance ne sakamakon Tsohon gwamnan na goyan bayan takarar daya daga cikin masu neman kujerar Shugabancin Jam’iyya Wato (Barrister Tanko Beji Da Eng. Mukhtar Ahmad)

Ku cigaba Da Bibiyar Shirin mu Ta NEJAR MU AYAU domin Jin Danbartuwa Akan Siyasar Jihar Neja.

Daga Abu Yaseer Shamsuddeen Yakaji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *