Kada Wani Jami’i A Gwamnatina Ya Kuskura Ya Ƙara Yiwa Majalisa Rashin Ɗa’a- Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargaɗi Ma’aikatu, Sassa da Hukumomi, MDAs, su daina raina Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Shugaba Buhari ya yi wannan gargaɗin ne awowi bayan Muƙaddashin Shugaban Hukumar Kula da Yankin Neja Delta, NDDC, Kemebradikumo Pondei, ya fice daga majalisa a lokacin da wani Kwamitin Bincike na Majalisar Wakilai yake tuhumar sa a kan wata badaƙala.

A yayin wata ganawa da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan da Shuagaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ranar Alhamis, Shugaba Buhari ya amince da rawar da Majalisar Dokoki ke takawa wajen gina ƙasa.

Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar ta ce Shugaba Buhari “yana matuƙar girmama Majalisar Dokoki ta Najeriya”.

“Ba za a lamunci rashin girmamawa ba kowane iri daga duk wani mamba na Majalisar Zartarwa.

“Ya kamata a koyaushe ministoci da dukkan shugabannin sassa su yi halin ɗa’a da ba zai nuna rashin girmamawa ba ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin cibiya, shugabanninta da mambobinta.

“Shugaban Ƙasa da shugabannin Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun aminta cewa Ɓangaren Zartarwa da Ɓangaren Majalisa na gwamnati abokan aiki na masu muhimmanci sosai a wajen sauke nauyinsu na inganta rayuwar ‘yan Najeriya”, a cewar Shugaba Buhari.

A zaman Majalisar Wakilai na ranar Alhamis, Kemebradikumo Pondei, Muƙaddashin Shugaban NDDC da wasu jamai’an gudanarwar hukumar suka fice a lokacin da wani Kwamitin Bincike na Majalisar Wakilai yake tuhumar su, bayan da suka dage cewa Shugaban Kwamitin bai kamata ya jagoranci zaman ba.

Mista Pondei ya ce Olubunmi Tunji-Ojo, Shugaban Kwamitin yana da hannu a badaƙalar NDDC ɗin, saboda haka bai kamata ya binciki badaƙalar da shi ma ana zargin sa da hannu a ciki ba.

Kwanaki kafin haka, an kori Festus Keyamo, Ƙaramin Ministan Ilimi daga wani taron tattaunawa na kwamitin Majalisar Dattijai, bayan wata zazzafar muhawara tsakaninsa da ‘yan majalisar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *