Jamhoriyar Nijar Ta Taso Ƙeyar ‘Yan Najeriya 42 Zuwa Gida

Rundunar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, NIS, a jihar Katsina, ta karɓi ‘yan Najeriya 42 da Jamhoriyar Nijar ta dawo da su sakamakon shiga ƙasar ba bisa ka’ida ba, a kan hanyarsu ta zuwa Turai.

Mai Magana da Yawun NIS a jihar, Sunday James, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Juma’a a Abuja.

Mista James ya ce an dawo da ‘yan Najeriyar ne ta Kongolam.

Ya ce ‘yan Najeriyar da aka dawo da su ɗin ‘yan shekara 18 zuwa 35, sun ƙaurace wa tantancewa da NIS take yi, suka ƙetara boda suka shiga Jamhoriyar Nijar.Adnairax

Ya ƙara da cewa wata Babbar Kotun Tarayya dake Katsina ta yanke wa mutum 12 daga cikin mutanen 42 hukunci sakamakon shiga Nijar ba bisa ka’ida ba, a hanyarsu ta zuwa Turai.

“Mai Shari’a Hadiza Shagari, a lokacin da take yanke hukunci, ta umarci waɗanda aka dawo da su ɗin ko dai su biya tarar N50,000, ko kuma a ajiye su a gidan gyaran hali na tsawon wata uku.

“Su ma sauran masu laifin 30 nan ba da daɗewa ba za a maka su a kotu da zarar an kammala bincike da ake yi a kansu”, in ji Mista James.

Da yake tsokaci a kan wannan al’amari, Shugaban Hukumar NIS na Ƙasa, Muhammad Babandede, ya bada umarnin a yi wa sauran mutanen 30 shar’ia ba tare da jinkiri ba.

Mista Babandede ya shawarci matafiya da su riƙa gabatar da kansu ga jami’an NIS don tantancewa duk lokacin da za su yi tafiya.

Ya kuma shawarci masu dawowa Najeriya da su ma su riƙa gabatar da kansu don tantancewa, kamar yadda Sashi na 15 Ƙaramin Sashi na (1) a d b na Dokar Shige da Fice ta 2015 ya tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *