Ingantaccen Maganin Cin Ruwa

Cin ruwa wani ciwone wanda ya addabi wasu jama’a, kuma mai wuyar magani, abunda zai baka mamaki akan wannan ciwon shine, wasu har ƙasashe waje sunfita don samun maganin wannan matsalar amma abun yaci tura.
Yanzu zan kawo yanda za’a hada maganin wannan matsalar cikin sauki da yardar Allah.

YANDA ZA’A HADA MAGANIN

Asamu ‘ya’yan bagaruwa ta Afirika wato ‘ya’yan bagaruwar Najeriya, kamaru da gana, ba bagaruwar maka ba. Sai adaka atankade.

YANDA ZA’A YI AMFANI DA MAGANIN

Inza’a kwanta barci abarbada garin maganin a kan ciwon, hakama washegari da rana abarbada garin maganin. Zuwa kwana uku.
In sha Allahu za’a warke tas daga wannan matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *