Masarautar Kano: Ganduje Ya Yi Magana Game Da Dawo Da Ciroma, Ɗan Agundi

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani game da zargin da ake cewa Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje yana da hannu a sake naɗa Aminu Babba Dan-Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba, da Sanusi Ado Bayero a matsayin Wamban Kano.

Labarai24 ta kawo rahoton yadda Masarautar Kano ta rubuta wasiƙa zuwa ga gwamnatin jihar Kano, don amincewa da naɗin tsohon Ciroman Kano, Sanusi Ado Bayero a matsayin Wamban Kano da tsohon Sarkin Dawaki Mai Tuta, kuma Hakimin Gabasawa Aminu Babba Dan-Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba.

Da suke bayyana ra’ayinsu game da wannan ci gaba, wasu mazauna Kano sun yi zargin cewa tun a baya, Gwamna Ganduje ya buƙaci tsohon Sarki Muhammad Sanusi II da ya mayar da Aminu Babba Dan-Agundi, amma tsohon Sarkin ya yi watsi da buƙatar.

A martaninsa, Babban Mai Ba Gwamna Ganduje Shawar Kan Al’amuran Masarautu, Tijjani Mailafiya Sanka, ya ce waɗannan zarge-zarge ba gaskiya ba ne.

Mista Sanka ya ce waɗanda suke cece-ku-ce game da wannan ci gaba mutane ne masu son ganin rikici yana afkuwa maimakon sulhu da yafiya.

“Ni ne wanda nake shiga tsakanin gwamnatin jiha da Fadar Masarautar Kano, kuma ina tabbatar muku da cewa ba wani lokaci da wannan abu ya faru.

“Ba zai yiwu ba a ce zaɓaɓɓen Gwamna ya buƙaci Sarki ya yi wani abu da ba ya cikin doka ballai kuma har a ce Sarkin ya ƙi”, in ji shi.

Mista Sanka ya ce waɗanda suke cewa Sarkin Kano ya saɓa wa mahaifinsa suna faɗar haka ne cikin jahilci.

Ya ce wannan ba shi ne lokaci na farko ba da za a cire hakimi daga sarauta bisa wani zargi, kuma a mayar da shi.

“Lokacin mulkin marigayi Ado Bayero, an cire Wamban Kano, Abubakar, kuma daga baya aka naɗa shi sarautar Ɗan Buram.

“Saboda haka, ba sabon abu ba ne, Sarkin yana bin sawun mahaifinsa ne kawai.

“Haka kuma, a lokacin Sarki Usman, an sauke Galadiman Kano na wancan lokaci, Mahmud, sakamakon wani laifi, daga baya kuma Sarkin ya sake naɗa shi a matsayin Magajin Gari”, ya ƙara da haka.

Mista Sanka ya ce waɗanda aka naɗa ɗin mutane ne masu tarin gogewa idan ana maganar masarauta, kuma suna da masaniya bisa abubuwan da suke faruwa a duniya, shi yasa Sarkin ya yanke shawarar amfani da tarin gogewarsu don bunƙasa masarautar da kuma jihar Kano gaba ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *