Majalisar Za Ta Binciki Dalilin Da Yasa Sojoji 365 Suka Ajiye Aikinsu

Rahotanni sun bayyana cewa majalisar wakilan Nijeriya sun jaddada bukatar gudanar da bincike a kan wani wasu sojoji 365 da suka ajiye aikinsu lokaci ɗaya.

Hukumomin sojin ƙasar dai sun ce akan bawa sojoji masu buƙata damar yin irin wannan murabus din daga lokaci zuwa lokaci amma `yan majalisar sun musanta, suna cewa ba a taɓa samun sojojin da yawansu ya kai bataliya sun yi ritaya karo ɗaya ba.

Hon Muhammad Tahir Monguno babban mai tsawatarwa a majalisar kuma shine ya gabatar da kudurin da majalisar ta amince don gudanar da bincike, ya shaida cewa matsaloli ne kawai suke tilastawa sojojin yin murabus.

A ƙarshen da ya gabata ne rahotanni suka ambato cewa sojoji 350 zasu ajiye aikinsu na soja saboda sun gaji da aikin bisa wasu dalilai na rashin gamsuwa da shugabancin rundunar.

Haka kuma ƙarancin albashi da rashin kayan aiki da ma rashin karfafa masu gwiwa na daga cikin batutuwan da ƙananan sojojin da ke yaƙi da Boko Haram suka koka a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *