Hantsarin Mota A Kaduna Ya Halaka Sojar Sama Mace Ta Farko Mai Tukin Jirgin Yaki

Hukumar sojin saman Nijeriya ta bayyana cewa ta yi rashin jami’arta mace ta farko mai tukin jirgin sama mai tashin ungulu, Flying Officer Tolulope Arotile, a wani hatsari da ya rutsa da ita jiya Talata a Kaduna.

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na hukumar sojin saman Nijeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana mutuwar hazikar sojan jiya a Abuja a wata sanarwa da ya fitar.

Tolulope ta rasu ne bayan da ta samu buguwa a kanta sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da ita a cikin barikin sojojin sama da ke Kaduna a jiya Talata 14 ga watan Yuli, 2020.

Kafin rasuwarta, Tolulope ce mace ta farko da ke da kwarewa a tukin jirgin saman yaki mai saukar ungulu.

An kaddamar da Tolulope a matsayin cikakkiyar sojan sama a shekarar 2017 bayan kammala karatu da horo a makarantar horar da sojoji ta Nigeria Defence Academy NDA.

A dan tsawon rayuwar aikinta, Tolulope ta bada gudunmawa matuka wajen yaki da ‘yan ta’addan arewacin Nijeriya ta hanyar kai farmaki akan ‘yan ta’addan yankin arewa ta tsakiya a karkashin rundunar Operation Gama Aiki da ke da shedikwata a Minna, babban birnin jihar Neja.

Marigayiya Tolulope Arotile ‘yar asalin garin Iffe ce da ke a karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi.

Babban Hafsan sojojin sama na Nijeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, a madadin kafatanin sojojin saman Nijeriya na mika ta’aziyyarsa ga iyalan Marigayiya Tolulope bisa rashinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *