An Yi Kira Ga Ma’aikatan Jahar Jigawa Da Kara Sanya Kishi Da Tsaron Allah Wajen Aiwatar Da Ayyukansu


Shugaban maaikata na jihar Jigawa Alhaji Husseini Ali Kila ya hori ma’aikatan jihar nan dasu kara sanya kishi da tsoran allah wajen gudanar da aiyukansu


Yayi wannan gargadin ne a lokacin taron farko da daraktocin mulki da kudi da jamian tafikar da mulki na maaikatu da hukumomin gwamnatin jiha da aka gudanar a babban taron taro na Sir Ahmadu Bello Hall dake sakatariyar gwamnatin jiha


Alhaji Husseini Ali Kila yace akwai bukatar maaikata su rinka zuwa wuraren aiyukansu akan lokaci domin cin gumunsi


Inda ya hori daraktocin dasu tabbatar da yiwa maaikatansu karin girma da sauran hidimomi da ake yiwa maaikata


Tun farko babban sakatare a ofishin shugaban maaikata Alhaji Umar Sule Gwaram yace an kira taron ne domin tataunawa kan yadda za a ciyar da alamurran maaikata gaba


Shima da yake jawabi babban sakataren sashen maaikata da bada horo Alhaji Ahmad Datti ya nanata kudirin gwamnatin jiha na cigaba da horas da maaikata domin inganta alamurran gwamnati


Wasu daga cikin mahalarta bitar sun bada tabbacin bada hadin kai da goyan baya domin cigaban aiyukan kwadago a jihar nan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *