An Naɗa Tsohon Shugaban Kasar Najeriya A Matsayin Jakadan Sasanta Rikicin Mali

An nada tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan a matsayin wakili na musamman da zai shiga tsakani domin ya sasanta rikicin siyasar da yake kokarin mamaye kasar Mali.

Wannann jagoranci da aka ba shi, ana sa ran zai tattauna da manyan masu fada a ji na kasar, ciki kuwa harda shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta, sai kuma shugabannin jam’iyyun hamayya, da kuma kungiyoyin fararen hula tare da Malaman addini domin ganin an shawo kan rikicin bai zama wani abu daban ba.

Kasar Mali ta fada cikin rikicin siyasar ne a makonnin da suka gabata, a inda masu zanga-zanga suka rika kiran shugaban kasar da ya sauka daga mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *