Kungiyar Izala ta kai tallafin kayayyakin masarufi ga ‘yan gudun hijira a jihar Karsina.

A litininin dinnan ne kungiyar JIBWIS ta kai ziyarar kwana daya a Jihar Katsina, domin jajanta musu mace mace da ‘yan ta’adda suka addabi jihar da shi, sannan ta kawo musu tallafin kayan masarufi domin agaza musu.

Tun farko a jawabinsa shugaban kungiyar Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cewa sun kawo wannan ziyara ne tare da yan tawagarsa domin sada zumunci tare da jajantama al’ummar Jihar Katsina saboda fitintinu da rashin zaman lafiya da ya addabi wannan Jiha da sace-sacen mutane, yan ta’adda iri daban daban da ke faruwa a wannan Jiha. Wannan ne ya sanya Kungiyar kawo wannan ziyara domin jajantawa tare da yin addu’a akan Allah ya gafarta ma wadan da mu ka rasa, wadan da kuma su ka rasa dukiyar su Allah ya mai da masu da mafi alkhairi, wadan da kuma suka samu ciwo, Allah ya ba su lafiya, sannan mu roki Allah madaukakin sarki yayi mana maganin yan ta’addan ya dawo mana da zaman lafiya a wannan Jiha ta mu da sauran Jahohin da ke fama da rashin kwanciyar hankali.

Sheikh Bala Lau Ya kuma kara da cewar sun kawo tallafi na Atamfofi da Shaddoji da sauran kayan masarufi domin rabama wadan da su ke a matsugunnin yan gudun hijira, amma bisa tsarin da Gwamnatin Jihar Katsina tayi na cewar duk Kungiyar da zata bada wani tallafi sai dai ta kawo ma Gwamnati, domin kauce ma 6ata gari da za su yi amfani da kai tallafi su kuma cutar da al’ummar. Hakan ya sanya Shugaban Kungiyar na Kasa ya hannata tallafin ga Gwamnan Jihar Katsina duk da cewar Gwamnan ya amince ma Shugaban Kungiyar ya kai da kai da kansa, amma Sheikh yace ya gode da wannan karamci amma saboda ganin an tabbatar da wancan tsarin zai hannanta kayan ga Gwamnan, domin a isar da su garesu kamar yadda aka tsara.

A karshe Sheikh Bala Lau ya jinjina ma Jihar Katsina akan duk da halin da ake ciki na rashin kwanciyar hankali Jihar tazo mataki na hudu (4) a wajen bada tallafin ginin Jami’ar As-Salam tare kuma da hadin kai da ake samu a duk aikin da ya taso.

Da yake mai da Jawabi, Shugaban Kungiyar na Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan ya bayyana jin dadin sa da wannan ziyarar da Shugaban JIBWIS ya kawo tare da yan tawagar sa domin jajanta mana akan halin da Jihar mu ta ke ciki na hare-haren yan ta’adda.

Sheikh Yakubu Ya kuma kara da godiya tare da fatan alkhairi ga Shugaban a bisa irin yadda yake gabatar da Shugabanci tare da kokarin samar da abubuwan ci gaba wanda za su taimaki addini da al’umma in da ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da Shugaban ya samu a shugabancin sa.

Bayan kammala taron, Shugaban Kungiyar na Kasa ya ziyarci Sheikh Habibu Yahaya Kaura domin duba lafiyarshi in da ya samu rakiyar Sakataren Kungiyar na Kasa Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe, Shugaban Kungiyar na Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan sai Darakta Protocol na Kasa Alh. Sabo Musa Hassan.

Tawagar da ta raka shugaba Sheikh Bala Lau, akwai shugaban Majalisar Malamai, Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Daraktan agaji na kasa, sheik Mustapha Imam Sitti, da sauran shugabanni da Malamai, da ‘yan agaji.

Muna fatar Allah ya karbi ayyukan da wannan kungiya mai albarka take gudanarwa. Amin

Jibwis Nigeria
22 Dhul Qa’ada, 1441
14 July, 2020

Daga: Yusuf Hassan Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *