Matasa Miliyan 4.48 Sun Nemi Aikin N-Power- Sadiya

Ministar Ma’aikatar Jin Ƙai, Kare Afkuwar Annoba da Walwalar Jama’a, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa kawo yanzu, kimanin ‘yan Najeriya miliyan 4.8 ne suka nemi aikin N-Power, a ci gaba da ɗaukar ma’aikata da shirin yake yi.

Idan dai za a iya tunawa, ma’aikatar ta buɗe shafinta na Intanet don ɗaukar ma’aikatan N-Power na Rukunin C a ranar 26 ga Yuni, 2020, a ƙarƙashin Shirin Walwalar Jama’a na Ƙasa, NSIS.

A cewar ma’aikatar, mutum 400,000 kawai za a ɗauke a Rukunin na C.

Sai dai kwana 16 da fara ɗaukar ma’aikatan, shafin na ya yi wa fiye da ‘yan Najeriya miliyan 4.48 rijista.

“Tawagata da ni kaina muna ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don tabbatar da sauyin @npower_ng cikin nasara. Kwana 16 kenan da buɗe shafin, mun karɓi buƙatun mutane miliyan 4.48”, Misis Farouq ta wallafa haka a shafinta na Twitter ranar Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *