Kungiyoyin Yaki Da Rashawa Sun Rubutawa Buhari Wasika Kan Yiwa Magu Ba Daidai Ba

Fitattun kungiyoyin kasa da kasa da ke yaki da cin hanci da rashawa, sun rubuta wasika ga shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari kan abin da suke kallo a matsayin rashin kyautatawa Ibrahim Magu da aka dakatar daga kujerar shugabancin hukumar EFFC.

A cikin wasikar ta hadin guiwa da aka rubuta a ranar 9 ga watan Yuli, kungiyoyin na kasa da kasa sun ce, abin da ke faruwa a Nijeriya ya shafi kasashen duniya, kuma Ibrahim Magu ya jajirce wajen gudanar da aikinsa.

Kungiyoyin da suka rattaba hannu kan wasikar sun hada da Re:Common da Corner House da Globalwitness, dukkaninsu daga nahiyar Turai, sai kuma HEDA ta Nijeriya.

Kungiyoyin sun ce, kudade da kadarorin satar da Magun ya kwato, wata alama ce da ke nuna cewa, ya dukufa wajen yaki da cin hanci da rashawa, sannan kuma yana da jajircewa a bakin aikinsa a cewar wasikar.

Wasikar ta cigaba da cewa, kawar da Magu daga kujerar shugabancin EFCC da suka danganta da siyasa, ya sa an diga ayar tambaya kan aniyar Nijeriya ta magance babban musabbabin koma-bayan kasar, wato cin hanci da rashawa.

Kungiyoyin hudu sun kasance kan gaba wajen sanya ido da kuma tona asirin rashawar da aka tafka a badakalar Malabu, inda har aka tuhumi manyan kamfanonin man fertur na Shell da Eni a Najeriya da Italiya.

Magu ya musanta aikata ba daidai ba, yayin da fadar shugaban Nijeriya ta ce, binciken tsohon shugaban na EFCC na nuni da cewa, gwamnatin Buhari ba ta nuna son kai wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *