HATTA MIJIN AURE ZAI IYA YIWA MATARSA FYAƊE

Dokar Nigeria ya fassara fyade a matsayin duk mace ko yarinya da aka sadu da ita ko aka sanya wani abu cikin farjinta ba tare da amincewar ta ba, sai saboda an yiwa rayuwarta barazana shi ma fyaɗe ne.

Dokar Arewacin Nigeria dake cikin kundin Penal Code sashi na 282 yace Fyade zai tabbata idan aka samu wadannan abubuwa:

1-Ba tare da amincewarta ba
2-Ba ta so ba, wato bata da ra’ayi
3-Idan an mata barazanan kisa
4- Idan an mata karfa-karfa
5-Saduwa da matar aure ta hanyar yaudara tsammaninta cewa mijinta ne
6-Marar hankali ce, ko kuma duk yarinyar da bata cika shekaru 18 ba ko da aurenta akayi aka sadu da ita to ya zama fyade.

Don haka ku daina ganin wai anyi wa wata babbar mace fyade tayi ciki ku zo kuna cewa wai ba fyade aka mata ba, zina tayi, dokar Nigeria bai kallon haka matukar yarinyar bata cika shekara 18 ba to fyade ne.

Ko matar aure tsakaninta da mijinta idan bata amince ba mijinta ya sadu da ita zata iya yin karansa a kamashi a tuhumeshi da laifin aikata fyade.

Akwai kundin dokar Nigeria Child Rights Act (CRA) na shekarar 2003 sashi na 31 sakin layi na (1) da na (2) na cewa:

Duk wanda ya sadu da yarinyar da bata cika shekaru 18 ba to ya mata fyade, kuma hukuncinsa shine daurin rai da rai a gidan yari, kuma dokar ya hada har da yaro namiji da bai kai shekaru 18 ba idan akayi Luwadi dashi.

Don haka gayu ku fahimci wannan, ku daina zuwa kuna yiwa yaran mutane ciki muddin ba su kai shekaru 18 ba fyade ne a dokar Nigeria ko da akwai amincewarta.

Sannan ga masu ganin laifin mu don muna yada mutanen da suke fyade, ina ganin idan ba sana’ar mutum bane fyade ba to bai kamata yaji haushin mu ba.

Tona asirin masu aikata laifin fyade shine daidai, domin hankalin shugabanni ya kai ga abinda yake faruwa don su dauki mataki, boye laifin fyade ba taimakon al’umma bane, ya zama wajibi a tona asirin masu aikata laifin fyade da Luwadi.

Rigar Yanci International, a Tsaye muke ƙyam wajen Ganin an tabbatar da hukunci akan duk wani mai aikata fyaɗe ko Luwaɗi, Hatta matan Da ke Kashe Mazajen su Dan kishi ko wani Dalili na Daban.

Madogara: Rigar Yanci International

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *