Allah Ya Yiwa Sheikh Dr. Umar A. Sade Rasuwa

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN

Allah ya karbi rayuwar Sheikh Dr Umar A Sade a safiyar yau bayan fama da yayi da doguwar jinya.

Shehin malamin kamin rasuwarsa shine babban limamin masallacin Jumaah na Al-Iman dake bayan Airport nan cikin garin Bauchi, kuma malamine a jamai’ar gwamnatin tarayya dake garin Kashere jihar Gombe.

Insha Allahu za’ayi sallar jana’izarsa bayan sallar La’asar a babban masallacin Jumaah na Gwallaga dake nan cikin garin Bauchi.

Amadadin Kungiyar Izala ta jihar Bauchi, shugaban kungiyar Alh. Muhammadu Inuwa Dan’asabe yana mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da yan’uwa da abokan arziki dama al’ummar musulmi baki daya bisa wannan gagarumin rashi.

Dafatan Allah ya jikansa ya gafarta masa yasa aljannar firdausice makomarsa.

JIBWIS Social Media
12/07/2020

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *