Korona Ta Yi Sanadiyyar Kashe Wata Hamshaƙiyar Sarauniya A Kasar Afirka Ta Kudu

Gidan sarautar Afirka ta Kudu ya tabbatar da rasuwar Sarauniya Noloyiso Sandile sanadin cutar Covid-19.


‘Yar uwa ce ga Sarkin Zulu Goodwill Zwelithini, kuma tana rike da sarautar amaRharhabe a gidan sarauta.


Sarauniya Noloyiso ta auri Sarkin amaRharhabe, Maxhoba Sandile, fiye da shekara har lokacin da ya mutu a 2011.
Daga nan ne ta zama sarauniya saboda danta, Jonguxolo Sandile, ya yi kankanta sosai a nada shi sarauta.


An kwantar da sarauniya mai shekara 56 a asibiti sanadin Covid-19, a cewar kafar yada labarai ta SABC.


Shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana ta a matsayin “mai kare al’adun kasar kuma shugaba mai kwazo ga al’ummarta”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *