Ina Da Masoya Da Dama Masu So Na Da Aure Amma Ba Ni Da Saurayi A Kannywood – Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa dana turanci da tauraruwar ke haskawa Rahama Sadau, ta ce ta ji kamar za ta mutu lokacin kullen korona saboda yadda take zaune wuri guda na tsawon watanni.

Ta bayyana hakan ne a hira ta musamman da Nasidi Adamu Yahaya a shafin BBC na Instagram.

“Lokacin kullen sai dai mutum ya yi ta yin kame-make. Ka yi karatu ya ishe ka, ka yi kallo ya ishe ka, ka yi chatting ya ishe ka,” in ji ta.

Ta ce kullen ne yasa ba a jin duriyarta kwana biyu.

Har ila yau Rahama ta ce ta ji babu dadi a lokacin kuma ta ji “kamar za ta mutu.”

Ta ce sana’arsu tana bukatar tara jama’a kuma yanzu an hana yin hakan saboda wannan annoba saboda haka a cewarsa korana ta fi shafar su fiye da kowa.

Rahama ta ce ta kammala karatunta, inda ta karanta fannin Human Resource Management a kasar Syprus.

Ta ce karatun ne ya sa ba ta iya ci gaba da harkokin fina-finanta ba gadan-gadan.

Tauraruwar ta ce tana iya magana da harshe uku Hausa, Turancin Inglishi da kuma Indiyanci.

Rahama ta ce mutane da dama suna son ta da aure,”yawanci sai dai na yi dariya ko kuma na ce na gode,” in ji ta.

Sai dai ta ce ita ba ta da wani saurayi a Kannywood a halin yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *