Gwamnatin Tarayya Ta Janye Batun Komawa Makarantu

Gwamnatin Tarayya ta janye umarnin da ta bawa makarantun sakandire da na firamare a fadin Nijeriya na su koma, domin daliban ajin karshe su samu damar rubuta jarabawar kammala matakin aji shida na sakandire, aji uku na sakandire da kuma aji shida na Firamare.

Idan ba a manta ba gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a fara rubuta jarabawar kammala babban Sakandare na WAEC daga ranar 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumba.

Gwamnati ta ce da zarar an kammala wannan jarabawa sai kuma a maida hankali wajen yin jarabawar NABTEB da NECO.

Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta umarci ‘yan aji shida na babban sakandare su koma makaranta domin shirin rubuta jarabawar WAEC.

Sai dai kuma a ranar Laraba, gwamnatin tarayya ta janhye wannan umarni na bude makarantun kasar da kuma rubuta jarabawar WAEC da ta ce za a yi a watan Agusta zuwa Satumba.

” Babu makarantar da za a yarda ta fara aikin don jarabawar WAEC. Gara ace dalibai sun rasa shekara daya na makaranta da ace sun afka hadadrin kamuwa da korona.

” Za a bude makarantu ne a lokacin da gwamnati ta gamsu cewa babu hadari ga yara, ba wai don hukumar shirya jarabawar WAEC ta shirya rubuta jarabawa ba.

” Ku duba ku gani, yau idan yaro daya ya kamu da Korona, zai yadawa yaran ajinsa cikin dan kankanin lokaci, haka kuma idan a dakunan kwanan dalibai ne cutar zata yadu kamar wutar daji. Tsakani da Allah, lokaci bai yi ba na bude makarantu. Yara fa ba su san bada tazara a tsakanin su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *