Dan Wasan Gaba Na Tawagar Super Eagles Ta Nijeriya Ya Kamu Da Cutar Korona

Dan wasa gaba na tawagar kwallon kafa ta Super Eagles da ke wakiltar Nijeriya, Paul Onuachu, ya harbu da cutar COVID-19 kamar yadda gwaji ya tabbatar.

Sai dai, sakamakon gwajin na abokan taka ledar Paul Onuachu ta kungiyar Genk ta kasar Beljiyum kuma ‘yan asalin kasar Nijeriya, Stephen Odey da Cyril Dessers ya nuna su basa dauke da cutar ta COVID-19

Dan wasan mai shekaru 26 da haihuwa shi ne dan wasan Super Eagles na farko da ya harbu da Coronavirus tun bayan bullarta a watan Fabrairu.

A ranar Talatar da ta gabatane dai aka yi gwaji ga kafatanin ‘yan wasan kungiyar ta Genk, amma a yayin da kowane daga cikinsu sakamako ya nuna ba ya dauke da COVID-19, sai shi Paul Onuachu ne kadai bai tsallake ba.

Paul Onuachu ya koma kungiyarsa ne a ranar 28 ga watan Yunin da ta gabata, bayan da rashin sauka da tashin jirage sakamakon barkewar Coronavirus ya rike shi a jihar Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *