Ana Zargin Shugaban Jam’iyyar APC Da Yiwa Kananan Yara Fyade

An Kama Shugaban Jam’iyyar APC Na Wata Gunduma A Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Ya Yi Yara Biyu Fyade

‘Yan sanda sun kama shugaban jam’iyyar APC na wata gunduma a karamar hukumar Obi dake jihar Nasarawa, Christopher Ogah da laifin yi wa wasu yara mata guda biyu fyade a gidansa dake cikin garin Obi.

Yara matan ba su wuce shekaru 12 da 13 ba, kamar yadda bincike ya nuna.

Shugaban karamar hukumar Obi, Alhaji Mohammed Oyimogo Oyigye, a yayin tabbatar da lamarin, ya kara da cewa shi ya kwaci Ogah daga hannun fusatattun matasan da suka kama shi daga bisani suka mika shi ga jami’an ‘yan sanda.

Ganau ba jiyau ba, ya bayyana cewa shugaban APC din ya yi aika-aikar ne a yayin da yaran suka shigo gidansa dibar ruwa, kuma ba wannan ne karon farko da ake zarginsa da aikata hakan ba.

Tuni dai kwamishinan ‘yan sanda na jihar Nasarawa Bola Longe ya bada umarnin tura shugaban APC din ga sashen binciken manyan laifuka dake garin Lafia babban birnin jihar ta Nasarawa domin ci gaba da bincike daga bisani a ingiza shi zuwa kotu domin fuskantar hukuncin da ya kamace shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *