An Shawarci Masarautar Kano Ta Naɗa Ganduje Sarautar ‘Jarman Kano’

Alhaji Abdullahi Umar Yusuf Maitama, ya shawarci Masarautar Kano da ta naɗa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Sarautar Jarman Kano.

Alhaji Maitama, wanda tsohon alƙali ne kuma zuri’ar Gidan Dabo ya bayyana cewar naɗa Gwamna Ganduje wannan sarauta zai taimaka wajen haɓbaka aikin noma a jihar Kano.

Maitama ya bayyana haka ne a cikin wani rahoton shirin in Da Ranka na Freedom Radio, shirin da Labarai24 ta bibiyi maimaicinsa ranar Alhamis.

A cewarsa, idan aka duba Jarman Kano na farko, Alhaji Adamu Ɗan Kabo, shahararren ɗan kasuwa ne, wanda har duniya ta naɗe ba za a manta da shi ba, saboda ƙoƙarinsa da kamfaninsa na jirage

Ya ƙara da cewa, sai kuma Farfesa Isa Hashim, wanda aka naɗa a matsayin Jarman Kano na biyu, shi kuma malamin makaranta ne, wanda ya shahara sosai saboda ilimi da ƙoƙarinsa na inganta tsarin ƙananan hukumomi a ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa idan aka yi duba a wannan lokaci, za a ga Gwamnan Kano ya hana bara, inda har aka mayar da almajirai ƙauyukansu, don haka naɗa Gwamnan a matsayin Jarman Kano na uku zai taimaka wajen haɓaka noma.

“Wannan gaɓa ce da Maigirma Gwamna zai yi amfani da ita, ya yi shugabanci na Jarman Kano, ya yi jagorancin noma, sarakunansa a ba ba su tantan a daidai wannan lokaci.

“Sannan su dagatai da masu unguwanni da limamai da su masu tsangayar da ake zancen yaransu, a dinga ba su keken shanu, za a ga a wannan daminar in shaa Allahu za a motsa”, in ji Maitama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *