Allah Ya Yiwa Shugaban Ma’aikatan Jihar Kwara Rasuwa Sanadiyyar Korona

Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana cewa Shugaban ma’aikatan fadan gwamnatin jihar, Abdulrahman Abdulrazaq ya rasu bayan fama da da ya yi da cutar Korona.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar Rafiu Ajakaye ya Sanar da haka ga manema labarai a ranar Talata da Yamma.

Ajakaye ya ce Abdulrazaq ya rasu bayan awowi da aka gabatar da sakamakon gwajin cutar da aka yi masa wanda ya nuna cewa ya kamu da cutar.

Gwamnati ta yiwa iyalen Abdulrazaq da mutanen masarautar Ilorin ta’aziyar rasuwar marigayin.

Ya ce nan ba da dadewa ba iyayen Abdulrazaq zasu sanar da ranar da za a yi jana’izar Abdulrazaq.

Kafin Abdulrazaq ya rasu ya rike mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati daga ranar 7 ga watan Yuni 2019.

Gwamnati ta bada kwanakin bakwai domin makoki da juyayin rasuwar Abdulrazaq.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *