Zaben Edo: Mu Ba Dala Ba Ce A Gabanmu- Jam’iyyar PDP Ga Ganduje

Jam’iyyar PDP ta yi wa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje shaguɓe bisa maganar da ya jefa wa Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Gwamna Ganduje, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kamge na APC a zaɓen gwamna na jihar Edo, ya zargi PDP da yunƙurin yin maguɗi a zaɓen na Edo, yana mai cewa Gwamna Wike, wanda shi ne Shugaban Kamfe na PDP “za a tura shi cibiyar killace kai”.

Amma a wata sanarwa da PDP ta fitar ranar Litinin, Sakataren Yaɗa Labaranta na Ƙasa, Kola Ologbondiyan ya ce abin dariya ne Gwamna Ganduje “wanda ya zama abin kunya a ƙasa bayan ganin sa yana karɓar dalolin Amurka a wani faifan bidiyo da ya bazu” yana zargin PDP da cin hanci.

Ya bayyana Gwamnan Kano a matsayin “mai wawashe lalita, wanda ba shi da ikon yin magana game da cin hanci”.

Mista Ologbondiyan ya ce amfanin lalitar jihar Edo shi ne a hidimta wa al’ummar jihar da ita, yana mai ƙarawa da cewa: “babu dalar kyauta gare shi (Ganduje) da sauran jagororin APC a jihar Edo da za su wawashe”.

“Abu ne mai rikitarwa yadda mutumin da ya jawo wa kansa abin kunya daga jama’a “gandollar” bayan an kama shi yana karɓar na goro zai riƙa yunƙurin zargin wasu da ƙoƙarin wawashe lalitar wata jiha”, in ji sanarwar.

A cewar PDP, a jam’iyya kamar APC ne kaɗai, a ƙarƙashin mulkin Buhari, za a iya zaɓar wannan mutumin ya yi jawabi a cikin jama’a, har ma ya jagoranci kamfe a zaɓen gwamna.

“A fili yake, Gwamna Ganduje da sauran jagororin APC sun saba da wawashe lalitar al’umma, yadda maganar da ya fara yi kenan bayan an rantsar da shi don ya jagoranci kamfe na zaɓen gwamnan jihar Edo.

“Gwamna Ganduje ya kuma tabbatar da cewa aniyar zahiri ta PDP, wadda ita ce su yi amfani da ɗan takararsu mara inganci, Osagie Ize-Iyamu (tabbas, halinsu ɗaya) yadda suka rikice don su samu mallakar lalitar jihar Edo, bayan Gwamna Godwin Obaseki ya ‘yanta jihar daga hannun iyayen APC masu wawashe lalita”, sanarwar ta ƙara da haka.

Mista Ologbondiyan ya ce ba za a iya kwatanta Gwamna Ganduje da Gwamna Wike ba.

A shekarar 2018, jaridar Intanet, Daily Nigeian ta wallafa wasu faya-fayan bidiyo inda aka nuna Gwamna Ganduje yana karɓar na goro daga hannun ‘yan kwangila, amma dai Gwamnan ya ƙaryata hakan, yana mai cewa faya-fayan bidiyon, waɗanda sun bazu kamar wutar daji, ƙirƙirar su aka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *