Za A Sake Garkame Nijeriya Da Lockdown Nan Da Mako 2 – Boss Mustapha

????????????????????????????????????

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar kulle ta hanyar ayyana ‘Lockdown’ nan da mako biyu masu zuwa.

Wannan kuwa na zuwa ne bayan da gwamnati ta fahimci cewa annobar COVID-19 na ci gaba da fantsama musamman ma a tsakanin masu rike da manyan mukaman gwamnati da ma iyalansu.

Shugaban kwamitin kar-ta-kwana kan yaki da annobar COVID-19 kuma sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan jiya Litinin, inda ya koka cewa annobar a yanzu na kokarin kawo cikas kai tsaye ga harkokin tafikar da gwamnati da ma tsaron kasar.

Boss Mustapha, a jawabin nasa na jiya ya bayyana cewa, abubuwan da za su faru a makonni biyu masu zuwa sune za su tabbatar da hukuncin da gwamnati za ta dauka kan ci gaba da sakin gari ko kuma sake garkame shi.

“Za mu mika rahoto ga shugaba Muhammagu Buhari kan sauki ko rashinsa nan da makonni biyu, shi kuma zai yanke hukuncin da ya dace,” inji Boss Mustapha.

Wannan kuwa na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa da na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, duk suka harbu da cutar ta COVID-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *