Siyasar Jigawa: Aminu Ringim ya saka zare da Sule Lamido

Tsagin jamiyyar PDP da Mallam Aminu Ibrahim Ringim ke shugabanta ya yi watsi da nadin mutane biyar biyar da aka yi a matsayin shugabannin riko na jamiyyar PDP na kananan hukumomin jihar nan 27.


Da yake ganawa da manema labarai a gidansa dake Dutse, Mallam Aminu Ringim ya zargi kwamitin riko na jamiyyar da lefin hada baki da tsagin tsohan gwamnan jiha Sule Lamido wajen nadin kwamitocin riko na jamiyyar PDP a kananan hukumomin jihar nan ba tare an tuntubi bangarensa ba

Yace kwamitin riko na jamiyyar na PDP na jiha ya nuna son kai wajen nada kantomomin mulki na jamiyyar a kananan hukumomi ta hanyar amincewa da mutanen da tsagin Sule Lamido ya gabatar masa ba tare da tuntubar bangaren sa baA ranar jumaar data gabata ne kwamitin riko na jamiyyar PDP na jihaya kaddamar da kantomomin mulki na kananan hukumomi da nufin tafikar da harkokin jamiyyar

Inda a jawabinsa na kaddamarwa, kantoman riko na jamiyyar Alhaji Umar Mungadi yace an nada kantomomin ne sakamakon karewar waadin mulkin kwamitin koli na jamiyyar kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulkin jamiyyar

Madogara: Labarai24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *