Saudiyya Ta Fara Rijistan ‘Yan Kasasshen Ketare Da Zasu Yi Aikin Hajji

Kasar Saudiya ta fara rajistar ‘yan kasashen ketare da zasu gudanar da aikin hajjin bana, tana mai cewa sune zasu kunshi kashi 70 na maniyyatar bayan ta dakile yawan maniyyatar sakamakon bullar annobar coronavirus.

Saudiyya ta ce maniyyata kimanin dubu guda da aikin hajjin bana ya riske su a cikin kasarta ne kawai za ta bari su gudanar da aikin na wannan shekarar da zai gudana a watan Yulin nan da muke ciki, akasin mutane miliyan biyu da rabi da suka gudanar da aikin a shekarar da ta gabata.

Ma’aikatar ta ce ‘yan asalin Saudiyya ne zasu cike saura kashi 30 na maniyyatan da zasu gudanar da aikin hajjin bana.

Za a yiwa wadannn maniyyata gwajin cutar coronavirus kafin su isa birnin Makka, kuma za a bukaci su killace kansu a gida bayan aikin.

Wannan ne karon farko a tarihi da Saudiyya ta dakatar da maniyyata daga wajen kasar gudanar da aiki hajji, lamarin da ya tada hankulan Musulmai a fadin duniya, sai dai da dama sun yi uzuri duba da ta’adin da cutar corona ke yi.

Mutane sama da dubu dari 2 da 13 ne suka harbu da wannan cuta a kasar, kusan 2000 suka ce ga garinku nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *