Naira N5,000 Aka Biya Ni A Matsayin Kudin Aikin Kashe Likitan Zamfara – Wanda Ake Zargi

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta cafke tare da yin holin daya daga cikin mutanen da ake zargi da kashe likitan nan na jihar Zamfara, Dakta Enoch Okpara, wanda likita ne na cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya da ke a Gusau wato FMC Gusau.

Wanda aka cafke din, Abubakar Namaliki, ya tabbatar da cewa an biya shi Naira dubu biyar ne kacal don ya gabatar da aikin kisa ga likita Enoch Okpara.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Barista Usman Nagogo, ya bayyana cewa an cafke Namaliki ne a cikin daren ranar Lahadin da ta gabata a cikin daji.

In ba a manta ba dai, a ranar 13 ga watan Yuni, 2020 ne dai wasu ‘yan ta’adda da ba a san ko su waye ba suka kutsa kai gidan Dakta Enoch Okpara da ke a garin Gusau, inda ba su yi wata-wata ba suka halaka shi suka kuma bankawa gawar tasa wuta.

Tun bayan faruwar al’amarin fa sai ‘yan sanda suka shiga fafutakar neman wadanda suka aikata wannan mugun aiki ka’in da na’in, kuma ba su yi nasara ba har sai a daren Lahadin da ta gabata, a cewar Kwamishina Nagogo.

Yanzu haka ‘yan sanda na nan na ci gaba da gudanar da bincike game da kisan, inda har Namaliki ya bayyana musu cewa shi da wasu mutum hudu ne suka aikata aikin kisan bisa
Namaliki ya bayar da sunayen abokan aikin nasa kamar haka: Alhaji Shehu Bagewaye, Iro Tsoho, Dan Hajiya (Smally), Auwali Banawa da kuma Muhammad Jansaidi.

A yayin da Namaliki ke magana da ‘yan jarida a yayin da ake holin nasa, ya bayyana cewa shugaban dabar tasu ya biya shi N5000 ne kacal a matsayin kudin aikinsa a kisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *