Kifewar Kwale-Kwale A Jihar Benuwe Da Legas Ya Lashe Rayuka Da Dama

Rahotanni sun bayyana cewa kifewar kwale-kwale a jihar Benue da Legas ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.

A jihar Benue ganau sun shaida cewa lamarin ya faru ne a karshen makon jiya inda kwale-kwalen da ke dauke da mutum 20 ya kife a kogin Benue.

Wani dan uwa ga wadanda hadarin ya rutsa da su, Phillip Amos ya bayyana yadda lamarin ya faru inda ya ce hadarin ya faru ne lokacin da jirgin da ke dauke da fasinjojin ya nutse.

A cewarsa, wani mutum ya rasa ‘ya’yansa guda biyar a hadarin jirgin.

Ya ce “abin ba sauki, bai zo da sauki ba gaskiya, yanzu duk muna cikin bakin ciki ne kawai.”

A jihar Legas kuwa, hukumomi sun ce kwale-kwalen ya kife ne ranar Juma’a bayan ya tashi daga Ebute-Ero a kan hanyarsa ta zuwa Ikorodu da daddare, abin da ya keta dokar hana tafiya da daddare.

Wata sanarwa da Dr Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Lagos ta fitar ranar Lahadi ta ce bincikensu ya nuna cewa fasinjoji 21 da matuka kwale-kwale biyu ne a cikinsa.

“An ceto mutum 16 (ciki har da matuka kwale-kwalen) da ransu yayin da mutum bakwai (dukkansu mata) sn rasa rayukansu,” a cewarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *