Zaben Edo: An aika Ganduje a matsayin Shugaban kwamitin yakin neman zabe na APC, PDP ta aika Wike

Jam’iyyar APC Ta Tura Gwamna Ganduje A Matsayin Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben, Jam’iyyar PDP Ta Tura Gwamna Wike

Kwamitin gudanarwa na kasa, NWC, na jamiyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta nada Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike a matsayin shugaban kwamitin yakin cin zaben gwamnan jihar Edo.

Jamiyyar ta kuma nada gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri a matsayin mataimakin rundunar cin zaben gwamnan.

Sakataren jamiyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Jumaa a sahihin shafin Twitter na jamiyyar.

NWC na @OfficialPDPNig ta nada @GovWike a matsayin shuganan rundunar cin zaben gwamnan jihar Edo.

Mataimakinsa kuma shine Rt. Hon. Ahmadu Fintiri,” kamar yadda ya wallafa a Twitter. Zaben Edo: APC ta tura Ganduje, PDP ta tura Wike.

Dan takarar jamiyyar, Gwamna Godwin Obaseki zai fafata da Osagie Ize Iyamo na All Progressives Congress da wasu yan takarar na wasu jamiyyu da za su fafata a zaben na ranar 19 ga watan Satumban a jihar.

Ologbondiyan ya ce, “Duba da cewa mutane jihar Edo suna tare da PDP da Obaseki, ba za su amince wani ya zo ya nemi sauya wa mutanen abinda suke so ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *