‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Shahararren Barawon Babur A Jigawa


Rundunar yansanda ta jihar Jigawa ta kama wasu matasa da ake zargin sun kware wajen satar Babura a sakatariyar gwamnatin jihar Jigawa dake Takur


A wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdu Jinjiri ya bayar ta bayyana sunan mutanen da suka hadar da Najib Salisu dake unguwar Tarauni a birnin Kano da Yusif Ibrahim dan KH Dala a jihar Kano da kuma Musa Nasiru dake zaune a Tudun Wada Kaduna


Mutanen uku da aka kama suna dauke da makulli na musamman da barayi suke anfani dashi wajen bude ababan hawa sun ce suna satar Babura daga wannan jiha zuwa waccan sannan kuma su sayar da baburan a kasuwanni


Sanarwar ta kara da cewar mutanen uku sun kuma tabbatar da cewar sun saci babur a sakatariyar gwamnatin jiha dake Takur
Yansanda suna cigaba da gudanar da bincike

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *