Rundunar Sojojin Najeriya Ta Yiwa Alumma Goma Na Arziki

Kimamin mutane sama da Dubu suka amfana da tallafin kayan abinci da hukumar sojojin kasar nan suka raba a karamar hukumar kauran Namoda dake Zamfara da Faskari a Jihar katsina a jiya Asabar da kuma yau lahadi.

Da yake gabatar da kayan tallafin ga wadanda suka amfana da shirin a garin kauran Namoda, Shugaban hafsan sojin Najeriya Laftanal janar Yusuf Tukur Buratai, ya ce wannan tallafin na daya daga cikin kokarin da rundunar sojin keyi na taimakawa marassa karfi, don su samu saukin yanayin da aka shiga sakamakon annobar Mashako.

Burtai wanda Shugaban sashen ingantawa da kirkirar sabbin dabarun yaki na hedikwatar rundunar dake Abuja manjo janar E. N Njoku ya wakilta, ya ce shekaru da dama rundunar na gudanar da tsare-tsaren ganin ta bada nata gudunmuwar.

Ya kara da cewa yana jinjinawa alummar jahar Zamfara baki daya, bisa ga cikkaken goyon baya da hadin kai da suke baiwa rundunar wajen yaki da ta’addanci a jahar,ya kuma bukaci alummar da su ci gaba da bada wannan hadin kai don cimma nasara.

Cikin Kayayyakin da aka raba sun hada da kananan buhunan shinkafa, da kayan shayi, da maggi, da ruwan roba, da kuma littafai duzun dubu Ashirin domin rabawa ga makarantu dake karamar hukumar Faskari da kauran Namoda.

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *