Ma’aikatan Hukumar NIPC Sun Nuna Farin Cikinsu Da Ritayar Wani Mugun Shugabansu (hotuna)


Ma’aikatan hukumar kula tare habbuka harkar saka hannu jari a kasar Najeriya (NIPC) sun nuna kwarai dagaske game da ritayar wani daya daga cikin daraktocin hukumar, Mr. Isaac Adesoola Idowu, wanda shine daraktan kudi na hukumar kafin ritayarsa.

Mr. Idowu kamar yadda Ma’aikatan hukumar a hotunar ban kwanarsa sun ayyana kamar haka; “ He will be fondly remembered for: high handedness, bigotry and wickedness, power drunkenness, disregard and disrespect for honest or hardworking staffs, lies and mischief, arrogance, witch hunting, fetishness and sadism, nepotism and tribalism.”

Wato

”Ba za mu taba manta da shi saboda wadannan dalilai kamar haka: mutum ne mai taurin kai, ga shi kuma mugu, wanda ya bar mulki ta rinjaye shi, sannan kuma mutum ne marawa ganin ma’aikata masu kokari da kuma gaskiya da mutunci, ya kasance mai makaryaci mai kitsa makirci, ga shi da girman kai da kabilanci da makamancinsu”

Lallai wannan ya nuna ma’aikata basu ji dadin aiki karkashin wannan shugaban ba tunda har suka kai ga yin haka; Allah ya sa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *