Labarin Attajirin Da Aka Kerawa Takunkumin Gwal Na Fiye Da Naira Miliyan N1 Don Kariya Daga Korona (hotuna)

Wannan attajiri mai suna Shankar Kurhade mai kimanin shekaru 49, mazaunin birnin Pune da ke yammacin ƙasar Indiya ya biya dalar Amurka dubu 4 ($4,000) daidai da kudin Najeriya Naira miliyan daya da dubu dari biyar da dubu hamsin da biyu, domin kera masa takunkumi na gwal don gudun kamuwa da cutar coronavirus.

Shankar Kurhade, ya ce ya samu bayar da aikin ƙera masa takunkumin na gwal bayan da ya ga rahoton wani da aka yiwa takunkumin silba. 

Attajirin dan kasuwar ya ce duk da ba shi da tabbacin takunkumin na gwal zai hanashi kamuwa da cutar korona, amma zai ci gaba da bin matakan kariya. 

Ƙasar Indiya dai ta sanya dokar amfani da takunkumin rufe baki da fuska, domin dakile yaduwar cutar korona a fadin ƙasar.

Haka kuma ƙasar tana da masu ɗauke da cutar korona kimanin 650,000 ya yin da kuma 18,600 su ka mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *