Gwamnan Jahar Ebonyi Dave Umahi Tare Da Mataimakansa Sun Kamu Da Cutar Korona

Gwamnan jahar Ebonyi, Dave Umahi, ya sanar da cewa ya kamu da cutar korona. Gwamnan ya sanar da hakan a wani sanarwa wacce takardar ya samu rattafa hannunsa a ka a ranar Asabar 4 ga watan Yuni, 2020.

A cewar gwamnan, ya ce an yi masa gwaji tare da wasu mataimakansa wanda gwajin ya nuna cewa gwamnan ya kamu da cutar a yayin da ya bayyana cewa Duk da cewa alamomin Da ke dauke da cutar bai fara nunawa a jikinsu, ya ce zai killace kansa kamar yadda hukumar NCDC Da kuma masana suka shawarta

Ya umurci mataimakinsa, Kelechi AIG we, Da ya shugabanci Shirye-shirye kare jahar daga yaduwa cutar a jahar Ebonyi. Ya yi kira fa al’ummar jahar Da su bi ka’idojin da hukumar NCDC ta bayyana wajen neman kariya daga cutar da muhimmanci sannan kuma ya ce zai fara gudanar da ayyuka sa daga gida.

A halin yanzu masu kame da cutar Wanda hukumar lafiya ta jahar ya tabbatar sun kai 438. An kuma sallami akalla mutane 357 a yayin da mutum 3 kacal suka rasa rayukansu sakamakon cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *