Gwamna Badaru Ya Amince Da Murabus Din Daya Daga Kwamishinoninsa


Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da murabis din kwamishinan lafiya Dr Abba Zakari wanda ya sami aiki a asusun kula da kananan yara na majalissar dinkin duniya UNICEF.


A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman Ga Gwamnan Jiha a Sabbin Kafafan sadarwa Auwal Sankara ya bayar tace kwamishinan mai barin gado ya taka rawar gani wajen inganta bangaren kiwon lafiya a jihar.


Sanarwar ta bayyana cewar gwamnati da alummar jihar nan sun yaba da irin gudunmawar da Dr Abba Zakar ya bayar wajen cigaban jihar nan ta bangarori daban daban


Haka kuma Dr Abba Zakar zai cigaba da zama kwamishina har zuwa wata mai zuwa inda zai fara da asusun UNICEF


Daga nan sai gwamnatin jiha tayi masa fatan alheri a sabon wurinsa na aiki da zai fara a watan gobe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *