COVID-19: Hukumar Alhazai Ta Jahar Jigawa Ta Mayarwa Maniyyata Kudadensu


Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa zata mayarwa da maniyatan aikin hajjin bana kudadensa na ajiya.


Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Sani Alhassan Muhammad ya sanar da hakan ga manema labarai a ofishinsa.


a wata sanarwa, inda yace hukumar ta kammala duk wani shiri na biyan kudaden ajiyar na maniyata


Yace sun sami umarnin hakan ne sakamakon taron da suka gudanar da hukumar aikin hajji ta kasa


Alhaji Sani Alhassan Muhammad ya kara da cewar wadanda suka biya kudaden su na ajiya suna zabin barin kudaden zuwa shekara mai zuwa ga wadanda suke shaawa


Yace gwamnatin jiha ta hannun hukumar ta nuna alhininta dangane da hukuncin da kasa mai tsarki ta dauka na hana zuwa aikin hajjin bana sakamakon bullar cutar corona virus

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *