Ban Ga Wanda Ya Isa Ya Hana Almajiranci A Najeriya – Ɗahiru Bauchi

Sanannen Malamin Ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya Shiekh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana rashin amincewarsa da gwamnonin Arewa bisa kokarin hana almajiranci da suke yi.

A hirar da jaridar The Sun tayi da shi, Sheikh Dahiru ya ce ana kokarin takewa mutanen da sukayi imani da shirin almajiranci hakkinsu kuma yana daya daga ciki.

Shehi ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowane dan kasa daman zuwa inda yaga dama domin yin addinin da yaga dama.
“Kundin tsarin mulkin kasa ya bamu ‘yancin yin addininmu duk yadda muka ga dama. Abinda mukafi girmamawa a addini shine AlKur’ani.” “Tun da addini ya basu dokokin da za’a bi amma suka ki biyayya, shin wani hakki suke da shi na ba Alkur’ani umurni? saboda haka, ba zamu yarda da haramta Almajiranci da gwamnonin Arewa sukayi ba.”

An take mana hakkin ‘yancin yin addininmu. Ba zamu amince a take mana hakkin zuwa kowane waje a kasar nan domin aiwatar da addininmu ba.” “Dalilin shine akwai gwamnati, kuma gwamnati na biyayya ne ga kundin tsarin mulki. Kundin mulkin tarayyar Najeriya ya ba ko wane dan kasa daman zuwa duk inda yaga daman yin addininsa.

Almajirai ‘yan Najeriya ne.” “Kwashe mana mutane tamkar dabbobi da kaisu wurare daban-daban da ake yi, ba zamu amince ba. A matsayinmu na ‘yan Najeriya, muna da hakkin yin addinimu. Alkur’ani ne abin farko a addininmu.” “Ba zamu amince a hana almajiranci ba.

Sheikh Dahiru Bauchi ya kara da cewa gwamnonin basu nemi shawarasu ba kafin haramta Almajirancin.

Inda baku manta ba kungiyar gwamnonin Arewa karkashin jagorancin gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ta yanke shawarar mayar da Almajirai jihohinsu na asali tare da haramta almajirancin gaba daya a Arewacin Najeriya.

Gwamnonin irin na Kano, Kaduna, Nasarawa, da Neja tuni sun alanta haramcin Almajirancin a jihohinsu A jihar Kano, akalla Almajirai 193 ne suka kamu da cutar COVID-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *