2023: ‘Dan Arewa Zamu Tsayar Takarar Shugaban Kasa- PDP

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa, dan Arewa zata tsayar takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Sanata Gebriel Suswan, tsohon gwamna jihar Benue ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da wakilin jaridar Sunnews.

”An tambayeshi kan cewa majalisar ta zama ‘yar amshin shatan Bangaren zartaswa, sai yace ba haka bane. Maganar gaskiya a baya an samu matsalar rashin hadin kai inda kasafin kudi sai ya kai har kusan tsakiyar shekara kamin a amince dashi shiyasa a wanan karin duk da cewa su suna bangaren hamayya ne amma suka bada hadin kai dan ci gaban kasa.

”Ya kara da cewa PDP ‘dan Arewa zata tsayar shugaban kasa a 2023. Yace a baya sun tsayar da ‘dan Arewa amma bai ci zabe ba dan haka har yanzu kujerar PDP ta shugaban kasa daga Arewa zata fito.

Wà Kuke So Jam’iyyar PDP Ta Tsaida A Matsayin ‘Dan Takararta A Zabe Mai Zuwa?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *