ZAMFARA: Buratai Ya Fito Da Sabon Atisaye Don Yakar Ta’addanci – Kanal Sagir Musa

Shugaban Rundunar sojojin Nageriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya fito da sabon Atisayi Wanda aka sakashi cikin bikin ranar sojoji da ke gudana a jihar katsina, hakan ya fitone Daga bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojojin Najeriya, kanal Sagir Musa a lokacin da yake yiwa manema labaru Karin haske kan abinda ake nufi da ranar sojoji Yau a jihar Zamfara.

Yace shirin Atisayen shirine da aka shigo dashi cikin wannan biki kuma Atisayi ne da za’a hada sojoji da kayan yaki domin a shiga dazukan da wadannan ‘yan ta’adda suke, har maɓoyar su Da ƙarfin tsiya.

Ya kara da cewa jihohin da abin zai shafa sune inda wadannan ‘yan ta’addan suke, kama daga Kaduna da Katsina da zamfara, Sakkwato da dai sauransu, domin kauda dukkan wadannan mutane Har maboyansu.

Cikin Jawabin Sagir Musa kan wannan biki na ranar sojoji, ya ce sun zo jihar katsina ne don gudanar da biki na shekara daya na tunawa da ‘yan mazan jiya, watau wadanda suka rasa rayukansu a wajan aiki.

Ya ce bayan wannan kuma suna tunawa da shekarun da hukumar sojoji ta kai a duniya, watau shekara Dari da hamsin da Bakwai(157) ya kuma ce duk hukumar da ta sami wadannan shekaru to lallai ya kamata a jinjina mata.

Daga: Shu’aibu Ibrahim Gusau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *