Yadda Wani Matashi Ya Bankawa ‘Yar Shekaru 14 Cikin Shege Ta Hanyar Fyade Sannan Ya Yasar Da Jaririn A Dajin Kauyen Sokoto


Rundunar ‘yan sanda reshen jahar Sokoto ta ce ta kama wani matashi, Shuaibu Aliyu, a kan zargin bankawa ‘Yar Shekaru 14 Cikin Shege Tare Da yasar da jaririn a daji.


Shi wanda ake zargi an kama shi ne bayan wani magidanci, Alhaji Abubakar, ya kai karar lamarin ga ofishin ‘yan sanda dake Wamakko a jahar.

An Gano cewa yarinyar ta dauka Ciki ne a cikin shekarar 2019 bayan Shuaibu ya ja ta zuwa dakinsa ya ma ta fyade.

Bayan ta haihu sai ta dau jaririn zuwa wurin wanda ake zargi sai shi kuma Tare Da abokinsa su ka dauka wannan jariri suka yasar Da jaririn a dajin dake kusa da kauyen Gidan Boka.

Kwamishinan ‘yan sanda na jahar, CP Sani Kaoje ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis. Inda ya kara da cewa an cafke shi wanda ake zargi da aikata laifin fyade Tare da yunkurin aikata kisa.

Kaoje ya ce “Wani magidanciwAlhaji Hamisu Abubakar Da ke yankin Kalambaina. A karkashin karamar hukumar Wanako a jahar Sokoto ya kawo rahoton a ofishin ‘yan sanda ake Wamako inda Yayi bayanin cewa a Cikin watan Nuwamba 2019, Shuaibu Aliyu, ya ja wata Yar Shekaru 14 zuwa dakinsa inda ya yi ma ta fyade.

“Sakamakon hakan yarinyar ta dauka Cikin shege. Sai ta dauka jaririn zuwa wurin matashin a yayin da ya zo ganin jaririn Tare Da abokinsa, Nasiru Attahiru, wanda ya tsere amma ‘yan sanda na nemansa ruwa a jallo, suka yasar da jaririn a.dajin kauyen Gidan Boka, dake karkashin karamar hukumar Wamakko a jahar Sokoto.”

Kwamishinan ya kara da cewa wasu bayin Allah sun tsinci jaririyar wadanda suka mika jaririyar zuwa gun hukumar karamar hukumar Wamakko sannan aka sanar da yan sanda.

Ya kara da cewa jami’an’yan sanda suna nan suna kokari cafke abokin wanda ake zargi wanda ya gudu domin har yanzu ana gudanar da bincike a kan lamarin kafin a mika Karan ga kotu .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *