Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haram Da Dama A Borno

A ranar Alhamis ne da misalin karfe 2:30 na rana mayaakan ƙungiyar Boko Haram suka shiga cikin garin Damasak, sun shiga garin ne da motocin yaki a kalla guda goma da kuma manyan makamai a hannunsu.

Jami’an sojojin Nijeriya sun yi fitar danko suka tunkari mayaƙan. Inda sojojin suka raunata su da dama tare da karbar akalla motoci uku na mayakan.

Daya daga cikin mazaunin garin na Damasak, ya ce babu shakka jami’an tsaron Nijeriya dake aiki a Damasak sun nuna bajinta, domin nuna rashin tsoron su da kuma fatattakar wannan mayaka da suka yi.

Kawo yanzu dai rundunar sojin kasar ba ta fidda wata sanarwa ba dangane da wannan nasara da suka samu akan kungiyar ta Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *