Da Duminta: Za A Yanke Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Ga Duk Wanda Aka Kama Da Laifin Yi Wa Yarinya Karama Fyade A Jihar Bauchi

A zaman Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi a ranar 30/06/2020 karkashin jagorancin shugaban Majalisar Rt. Hon Abubakar Y. Sulaiman aka bijiro da wannan batu kan fyade.

Hakan ya biyo bayan muhawara mai zafi ne dai Majalisar ta yi daga bisani ta amince da hukunci kamar haka:-

1 Duk wanda aka kama ya yi fyade ga karamar yarinya wacce ba ta balaga ba, za a yanke masa hukunci kisa ta hanyar rataya.

  1. Duk wanda aka kama yayi fyade wa mace wacce ta balaga (Ba Bisa yardar ta ba) za a yanke masa hukunci zama na dindindin a gidan yari.
  2. Dan gane da batun yin kaciya wa ‘Ya’ya Mata, Majalisar ta zartar da doka cewa duk Wanda aka samu da yin kaciya Wanda ya shige ka’ida zai tafi Gidan Kaso na shekara biyu ko zabin biyan Tara ta kudi Naira Dubu Dari Daya (100,000) ko Kuma yayi duka biyu (Ya biya tarar Kuma yaje Gidan yarin na shekara biyu).
    Da Kuma Sauran wassu hukunci dake tattare da wannan

Da yake zantawa da manema labarai Jim kadan bayan kammala zaman Majalisar shugaban kwamitin Ma’aikatar Mata ta Jihar Bauchi Hon. Wanzam Muhammed yace daukar matakin da Majalisar tayi ya Zama Mata wajibi Lura da irin cin zali da masu aikata aika-aikar keyi.

Ya lara da cewa a yanzu dai su a matakin su na “Yan majalisu (Majalisar) sunyi abinda zasu iya yi saura su jira amincewar Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala A. Muhammad ya Sanya hannu akan kudirin dokar.

Hon. Wanzam ya mara da cewa idan Allah ya amince wannan mataki da suka dauka a Majalisar zai kawo raguwa ko karshen wannan cin zarafi na fyade da akewa ‘ya’ya mata.

Ya kara da cewa a Majalisar ba a taba yin doka mai karfi kamar wannan ba lura da girman abin, da kuma masana harkar Shari’a da aka Kira da Kuma masu Kare muradun Dan Adam Wanda suka bada muhimman shawarwarin da ya dace Kuma akayi amfani dashi.

Ko Yaya kuka kalli wannan Dokar?

Daga: LDB

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *