Da Ɗumi-duminsa: An Kama Wanda Ya Saci Wayar Alkaliya A Jihar Ebonyi

‘Yan Sanda a jihar Ebonyi sun kama wani matashi me shekaru 20, Obiemezie Chiekezie da zargin sace wayar wata Alkaliya.

Mai Shari’a, Mrs. Ezeugo Esther na atisaye inda take sassarfa a bakin titi, nan ne marashin ya warci wayarta ta runtuma da gudu.

An dai yi kokarin kamoshi amma abin ya faskara. Saidai da aka bibiyi wayar an ganota a hannunshi inda aka kamashi ranar Laraba. An gurfanar dashi ranar Juma’a

Da yake bayyanawa kotu laifin wanda ake zargi, Dan sanda, Sabastine Alinona ya bayyana cewa, ya kwace wayar kirar Samsun x20 da darajarta ya kai Naira 180,000 ya ruga da gudu.

Babu dai lauyan da ya wakilci wanda ake zargi. Amma mai shari’a Mrs Nnenna Onuoha ta bada binsa akan Naira Miliyan 1 da kuma wanda zai tsaya masa mutum 1 wanda shima yana da wannan kudin, sannan kuma yana gida a inda karfin ikon kotun yake.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *