Kanin Mijin Matar Da Ta Yanke Azzakarin Mijinta Ya Bayyana Sunata Da Dalilin Da Ya Ta Aikata Hakan

Mun samu cikakken labari game da mata mai juna biyu wacce ta yanke azzakarin mijinta

Wani likita 1 ga watan Yuli ya bayyana yadda wata mata mai dauke da juna biyu ta yanke mazakutar maiginta da wuka bayan sau samu wani matsala a tsakaninsu.

Identity of pregnant woman who chopped off her husband

Aka zo aka sanar da ranar da abun ya faru inda aka bayyana cewa abun ya faru ne a ranar Laraba da safe 1 ga watan Yuli a wani kauye mai suna Tella da ke karamar hukumar Gassol a jahar Taraba.

Wata mata yar shekaru 32 ta mai suna Halima Umar tare da mijinta Aliyu Umar.

Dan uwar mijin matar, Usman Umar, ya ce babban yayansa ya kasance yana bacci ne a daki daya da uwargidansa wacce ta kasance matarsa na farko, Halima, yayin da ta tashi da tsakar dare da misalin karfe 2:00 na dare ta yanke masa azzakari.

Usman ya bayyana cewa matar yansa Aliyu Umar, sai ta sanya masa kwayar bacci a cikin abincinsa ta tabbatar da cewa ya kwanta bacci sannan ta aikata wannan mummunar aiki na yanke masa azzakari

Usman ya kara da cewa Halima ita ce matan yansa na farko sannan kuma sun kasance suna samu matsala tare da maigidan na ta tun daga ranar da ya sake yin sabuwar amarya shekaru 3 da suka wuce.

“Halima ta ci agba da hurawa maigidan na ta wuta, da shi da sabuwar amaryar nasa kullun a cikin fada suke duk cikin shekaru 3 da suka wuce,” inji shi.

Usman ya ce an kai yansa zuwa babban asibitin jahar dake Jalingo daga kauyen Tella domin a yi masa maganin ceto ransa. Daga nan ne aka garzaya da shi zuwa babban asibitin jahar Gombe.

Halima a nan take ‘yan sanda suka cafke ta sanna kuma aka mika ta zuwa hedikwatar yan sanda na wannan yankin wanda ke Mutum-Biyu a karamar hukumar Gassol.

Halima ta kasance tana da yaro namiji sannan kuma tana dauke da juna biyu watanni 8 a lokacin da aikata wannna mummunar aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *