Ganduje Ya Sake Rage Albashin Ma’aikatan Kano

Duk da cimma matsaya da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC, Reshen Jihar Kano, gwamnatin jihar Kano ta ƙara zaftare albashin ma’aikatan Kano na watan Yuni, kamar yadda jaridar Intanet, Nigetain Tracker ta wallafa.

Wasu ma’aikata da suka yi magana da jaridar bisa sharaɗin kar a bayyana sunansu sun ce an zaftare musu albashinsu na watan Yuni.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan ya ce a watan Mayu, a matsayinsa na ma’aikaci dake kan Matakin Albashi na 10, gwamnati ta zaftare N9,600 daga albashinsa.

“Mun saki jiki muna jiran albashin Yuni, abin mamaki aka zaftare N7,600 daga alabshina”, in ji wani ma’aikaci.

Wani ma’aikacin shi ma da yake aiki a Hukumar Ilimin Firamare ta Jiha, SUPEB, ya bayyana cewa an zaftare N3,000 da aka ƙara musu a watannin Mayu da Yuni.

Jaridar ta Nigerian Tracker ta gano cewa malaman firamare sun samu ƙarin N3,000 ne kawai lokacin da gwamnatin jihar Kano ta fara biyan mafi ƙarancin alabshi.

A lokacin da aka tuntuɓi Shugaban NLC na Kano, Kabiru Ado Minjibir a kan wannan batu, an samu wayarsa a kashe, kuma har yanzu bai bayar da amsa ba ga rubutaccen saƙon da aka tura masa.

A kwanan nan ne NLC ta Kano ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi bisa zaftare albashin ma’aikata na watan Mayu.

Daga baya kuma sai ta yi watsi da shawarar shiga yajin aiki, tana mai lura da cewa an cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *