Ba Aikin Mu Bane Fallasa Masu Daukar Nauyin Mayakan Boko Haram Ba – Rundunar Sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ba aikinta bane fallasa sunayen wadanda ke dauakr nauyin mayakan Kungiyar Boko Haram.

A yayin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar 2 ga watan Yuli, 2020, Shugaban Yada Labarai Na Ayyukar da suka shafi tsaro na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya ce duk da cewa sojojin Najeroya sun san da cewa wasu kungiyoyi ne ke daukar nauyin wadannan ‘yan ta’addan ba aikinta bane fallasa sunayen wadannann mutanen ba.

A cewar Enenche, aikin hukumomin tsaro na lekan sirri ne kamar su NIA da kuma hukumar tsaro na farin kaya wato DSS furta sunayen masu daukar nauyi wadannan mayakan.

“Makaman da wadannan mayakan ke amfani da su kamar su motoci masu dauke da bindigogi da irin makaman yakin da suke amfani da su duk masu tsada ne sannan kuma nawa suke sata har da za su iya sayen irin wadannan makaman, babu shakka hakan ya sanya mu ka san da cewa wasu manya ke daukar nauyin su” ya ce.

But like I said, it is not the duty of the military to uncover the sponsors.

Amma kamar yadda na fadi ne, ba aikin mu bane fallasa masu daukar nauyi wadannan mayakan.

Muna da hukumomin tsaro mai su leken asiri kamar su NIA da DSS duk aikin su ne wajen nema tare da fallasa wadannan mutanen ba aikin sojoji bane.’ Enenche ya ce.

Ya kara dda cewa sojojin Najeriya suna samu nasaran waje yaki da ta’addanci da rashin tsaro a fadin kasar.

“A yankin Arewa maso gabashin Najeriya takarun sojojin Najeriya dake aiki karkashin Operation Lafiy Dole (OPLD) sun samu nasara sosai wajen yakar mayakan Boko Haram a makonni 2 da suka gabata. A wannan lokacin ne, dakarun sojojin ne suka tararrasa mayakan a wurare daban daban tare da lalata kayan yakin mayakan tare da kwace wasu makaman mayakar.

A tsakanin ranaku 18 zuwa 30 ga watan Yuni, 2020 dakarun sojojin Najeriya na Operation Lafiya Dole sun sakarwa mayakan bama-bamai a dajin Sambisa dake jahar Borno bayan an gudanar da bincike a kan inda suke buya.

Hakan ya sanya sojoji suka lalata inda mayakan ke buya don shirya ayyukan ta’addancinsu a kauyukan Garin Maloma da kuma Yuwe. Kari, sojojin saman Najeriya sun bam-bame inda mayakan ke buya a kauyukan Buka Korege, da Bula Bello, da Ngoske, Tongule, da Bukar Meram da kuma Warshale inda aka lalata motocin bindigogin da kuma makamansu da dama.” inji Enenche

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *