Almajirai 193 Sun Kamu Da Cutar Korona A Kano

Akalla almajirai 198 A jahar Kano sun kamu da cutar korona a cewar gwamnatin jahar Kano.

A yayin da ya ke magana da manema labarai a kan korona a ranar Alhamis 2 ga watan Yuni, kwamishinan ilimi na jahar Kano, Sanusi Mohammed Kiru, ya bayyana cewa akalla mutane 1860 sun harbu da cutar korona a fadin jahar sanann dukkansu an killace su a wurare 3 daban daban a fadin jahar inda mutane 193 daga cikinsu suna kame da cutar.

Sanusi Wanda shine Shugaba kwamitin dake kula da abubuwa almajirai na jahar, ya cewa 86 daga cikin almajiran an killace suna a sansanin killacewa dake Gabasawa, da wasu kuma 68 Suna killace a Karaye a yayin da wasu 38 suke a sansanin Kiru.

Ya nuna farin cikinsa na yadda aka killace almajirai a jahar, karawa Da cewa Gwamnatin ta yi iya kokarin ta wajen ganin cewa cutar ba ya yadu a kauyukar jahar Da dama ba.

Ya tuna da cewa Gwamnatin jahar ta mayar da almajirai kusan 1183 zuwa Jihohin su na asali kamar su Jigawa , Kaduna Da makamancinsu kamar yadda gwamnonin arewa suke yanke hukuncin Kawo Karshen bara a Arewacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *