Kotu Ta Yi Watsi Da Karan Da Aka Mika Ma Ta A Kan Oshiomole

Wata babbar kotu dake gudanar da zamanta a Jabi a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da karar da aka mika a kan tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, tare da wasu mutane 3

Karar wanda wani dan siyasa, Comrade Mustapha Salihu tare da wasu mutane 5 suka mika kotu ita ta sanya kotu ta dakatar da Oshiomole daga kujerarsa na mulki a jam’iyyar

Lauyar da ya mika karar tsohon shugaba jam’iyyar, Oluwola Afolabi, wanda shi kuma ya sanya kotu ta yi watsi da karan da aka mika ma ta a ranar Alhamis 2 ga watan Yuni, ya ce hakan ya cancanta sakamakon tattaunawar da shugabancin jam’iyyar ta yi game da janye duk wani kara da aka mikawa kotu don wanzar da zaman lafiyar jam’iyyar

Lauyar Oshiomole, Ginika Ezeoke, ba ta yi gardama da hakan ba, yayin da ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar da ta aka mika ma ta a kan tsohon shuagaban jam’iyyar

Mai shari’a, Danlami Senchi, wanda shi ya jagoranci shari’ar a karshe yayi watsi da karar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *