Zamfara: Sojojin Sun Ceto Mutane 17 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

Aƙalla  Mutane 17 ne, aka samu nasarar ƙwato su daga hannun masu garkuwa da mutane biyo bayan wani sumame da rundunar soji suka kai a Jihar Zamfara.

Mutanen da aka kuɓutar daga hannun masu garkuwan ‘yan asalin jihar Sakkwato, kuma an miƙa su ga gwamnatin jihar ta Sakkwato.

Da yake karɓarsu, Gwamna Aminu Tambuwal ya yi farin cikin kasancewarsu cikin ƙoshin lafiya tare da godiya ga Gwamnatin Zamfara a kan ƙoƙarin da take yi.

Tambuwal ya kuma jaddada kiransa ga jama’ar jihar Sokoto da su ba wa jami’an tsaro haɗin kai wajen kawo karshen ayyukan  ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.

A cewarsa, gwamnatinsa a shirye ta ke da ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi al’umma.

Kwamishina samar da ayyuka da tsaron jihar Sakkwato, Garba Moyi, ya ce 16 daga cikin waɗanda aka kuɓutar sun fito ne daga ƙaramar Hukumar Tureta, mutum ɗaya kuma daga Rabbah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *